Mune ‘ya’yan jam’iyyar NNPP ta asali, Alhassan Rurum yayi fatali da dakatarwar da jam’iyyar NNPP ta yi masu a Kano


Dan majalisa mai wakiltar mazabar Rano, Kibiya, da Bunkure a majalisar wakilan Nijeriya, Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ya yi watsi da dakatarwar da aka yi masa daga jam’iyyar NNPP a Jihar Kano.Da yake mayar da martani kan sanarwar dakatarwar da shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ya fitar, Kabiru Alhassan Rurum ya ce shi da takwarorinsa da aka dakatar ba su taba bin bangaren da suka sauya tambarin jam’iyyar ba, yana mai jaddada cewa suna cikin jam’iyyar ta asali.