Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Wudil, Abubakar Abdullahi Likita, ya fadi ya rasu a daidai lokacin da ake gudanar da sallar jana’izar abokinsa kuma abokin siyasar sa, tsohon shugaban Karamar Hukumar Dala, Mahmoud Sani Madakin Gini.

Rahotanni sun bayyana cewa Likita ya fadi ne a lokacin da ake gudanar da sallar jana’iza ta Madakin Gini, lamarin da ya jefa jama’ar da suke wajen cikin firgici.
Za ayi janazarsa a talatar nan da misalin karfe 10 na safe a gidansa dake bomfai kusa da hedikwatar Immigration.Allah ya gafarta musu gaba daya.