Mun Hasaso Hoton Rayuwar Manzon Allah S.A.W A Ziyarar Da Muka Kai Kogin Hira, Cewar Shugaban Hukumar NAHCON


Shugaban hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan tare da tawagarsa sun kai ziyara ta musamman yankin Kogin Hira a garin Makkah, wanda ke zaman ɗaya daga cikin ɓangarorin da suka shafi rayuwar Manzon Allah S.A.W wajen samun nutsuwa da ibada, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.
Kamfanin sufuri na Mashaariq Al-Dhabia shi ne ya ɗauki tawagar wakilan hukumar ta NAHCON zuwa ziyarar domin su samu damar ganin yankin na Kogon Hira mai cike da tarihi, inda a nan ne aka fara saukar da Alƙur’ani mai girma ga Manzon Allah, S.A.W.
Da yake gabatar da jawabi a yayin ziyarar, shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, ya bayyana muhimmancin da ke tattare da ziyarar wajen mai cike da tarihi tun daga kan Annabi Adam zuwa Nuhu, Ibrahim, har zuwa kan Manzon Allah S.A.W. Ya bayyana wajen a matsayin waje mai tarihi da jin-daɗi.
Manzon Allah S.A.W yana ziyartar wajen shi kaɗai ya shafe tsawon dare yana bautawa Allah har zuwa lokacin da ya koma wajen matarsa. Mun shaida wannan waje da Idonmu, hakan ya taimaka mana wajen hasaso rayuwar Manzon Allah, gwagwarmayarsa da kuma yadda aka ba shi Annabta”. Ya ce.
Ya kuma ƙara da cewa, wannan ziyara za ta bar wani hoto na dindindin na ƙarfafa imani a zukatan alhazan da suka halarci wajen. Ya kuma yaba wa kamfanin sufurin na Mashaariq Al-Dhabia bisa wannan babbar ƙofa mai daraja da suka buɗewa alhazan Najeriya domin su ganewa Idonsu haƙiƙanin tarihin musulunci.
Wannan ziyara za ta ƙara sanya tsoron Allah da yaƙini a zukatan duk waɗanda suka halarta”. Ya ce.
Da bisani kuma, a yayin liyafar da aka shiryawa wakilan tawagar hukumar ta NAHCON da Yamma, Farfesa Pakistan ya yi yabo da godiya na musamman ga hukumomin ƙasar Saudiyya bisa shugabanci da suka gudanar mai cike da hangen nesa wajen gudanar da aikin Hajjin bana, 1446. Ya yaba da irin matakan tsaron da aka ɗauka da yadda aka tsara karɓan alhazai. Wanda a cewarsa komai ya tafi cikin nasara.
Hukumomin ƙasar Saudiyya sun ɗauki dukkan wasu matakai na kare dukkan wani abu da zai haifar da damuwa ga alhazai. Sun ɗauki tsauraran matakan tsaro, sun samar da wadatattun kayan amfani, an tsara komai yadda ya dace. Wannan ya nunawa Duniya cewa za a ci gaba da samun ci gaba na zamani sannu a hankali a kowane fanni na lamuran musulunci”. In ji shi.
Shugaban hukumar ta NAHCON, ya kuma ƙara da yabo da jinjina ga shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Sanata Kasheem Shettima dangane da gagarumar gudunmawarsu da cikakken haɗin-kai da goyon bayansu wajen samun nasarar aikin Hajjin bana.
Ya kuma yaba wa tawagar hukumar ta NNAHCON, musamman Musa Al-Hamed bisa nusarwarsa da gudunmawarsa wajen samun nasarar aikin. “Muna roƙon Allah Ya ci gaba da ɗora mu a kan daidai, Ya ce.
Shi ma a nasa jawabin, wakilin kamfanin Mashaariq Al-Dhabia, cikin girmamawa ya yaba da yadda kamfanin nasu yayi jigila da alhazan Najeriya, ya bayyana haɗin gwiwar a matsayin wani abun alfahari. Ya kuma ƙara da cewa ɗabi’a ta gari da alhazan Najeriya suka nuna abar misali ce.
Ya kuma ƙara da godewa shugabancin hukumar ta NAHCON bisa yadda suka ba da amanna da yaƙini a kan shugaban majalissar kamfanin Mista Adnan Mandoura da kuma shugaban gudanarwar kamfanin Mista Waleed Rasheedi, waɗanda ba su samu damar halartar wajen ba saboda yanayi na aiki da suka fita. “Wannan dama ce da muke fatan ci gaba da ɗorewarta a shekaru masu zuwa”. Inji shi.