A makon nan matatar Dangote ta sanar da shirin fara raba mai kyauta a Najeriya.

‘Yan kasuwa da dama sun nuna fargabar cewa shirn zai kawo musu cikas.

Masana tattali sun bayyana fa’idar da ‘yan Najeriya za su samu a karkashin shirin.

FCT, Abuja – Matatar Dangote ta bayyana cewa sabon tsarin da za ta kaddamar na rarraba mai fetur da dizil zai taimaka wajen rage hauhawar farashi da kuma kara ayyukan yi a fadin Najeriya. A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Talata, ya bayyana cewa tsarin zai bai wa masu gidajen mai, kamfanonin sadarwa damar samun kaya cikin sauki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *