Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya dawo gida Kano a yammacin yau Laraba Inda ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano bayan gudanar da Ibadar aikin Hajjin bana.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya dawo gida Kano a yammacin yau Laraba Inda ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano bayan gudanar da Ibadar aikin Hajjin bana.
Abba Kabir Yusuf ya shafe mako biyu a Kasa mai tsarki yayin da ya kasance Amirul Hajji na Jihar Kano.
Gwamnan ya samu tarba daga manyan jami’an Gwamnatin Kano ,shugabannin Kananan Hukumomi da masu bashi shawara da sauran magoya baya da suka fito daga sasssan Jihar Daban-daban.