Gwamnatin Shugaba Tinubu Ta Gina Akalla Tituna Da Nisan Su Yakai Kilomita 150 A Garuruwan Wajen Gari Dake Abuja, inji Wike

Ministan Abuja Nyesom Wike, ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da sabon titin da yataso daga A2 Junction akan hanyar Abuja–Lokoja zuwa Garin Pai a Karamar Hukumar Kwali dake Abuja, wanda yana daya daga cikin ayyuka 17 da aka aiwatar domin bikin cikar Tinubu shekaru biyu a kan mulki.
Wike ya ce aikin ya hada da tituna da aka kammala da kuma wadanda ake gudanarwa, domin kyautata rayuwa da ababen more rayuwa a garuruwan wajen gari. Titin A2 zuwa Pai mai tsawon kilomita 15 an gina shi ne a matsayin gaggawa, yayin da aikin titin Pai zuwa Gumani mai tsawon kilomita 15 akeci gaba da aiki, sannan an kuma bayar da kwangilar titin Gumani zuwa Yangoji mai tsawon kilomita 13, wanda zai kai jimillar kilomita 45 a yankin.
Ministan ya tuna cewa Tinubu ya amince da hanyoyi shida na gaggawa a cikin kananan hukumomi shida na Abuja a kasafin kudin 2024, kuma duka an kammala su. Wadannan sun hada da:
9km Paikon Kore zuwa Ibwa (Gwagwalada)
7.2km Gaba zuwa Tokulo (Bwari)
5km titin cikin birnin Kuje
11km Sukuku zuwa Ebo zuwa Yangoji (Kwali)
5km hanyar Saburi I da II (AMAC)
5km hanya a Abaji
Domin shekarar 2025, an shirya kaddamar da karin tituna, ciki har da:
10km titin Aguma Palace, da Radio Nigeria da kuma kasuwa a Gwagwalada
18km hanyar Nyanya zuwa Karshi
7.4km hanyar Dutse Alhaji zuwa Usuma Dam
16.4km hanyar Ushafa zuwa War College da Army Checkpoint
Da sauran hanyoyi a Bwari
Wike ya bayyana cewa wadannan tituna na da matukar muhimmanci wajen inganta rayuwar jama’ar karkara, bunkasa tattalin arziki, da kuma karfafa tsaro a yankunan.