Ana Raɗe Raɗin Matsafa Sun Shigo Unguwar Dawakin Dakata

Ana Raɗe Raɗin Matsafa Sun Shigo Unguwar Dawakin Dakata Wanda Suke Neman ƙananan Yara Wanda Basu Haura Shekara Biyar Ba Inda Suke Gutsire Musu Al’aurar Su.

Wanda Yanzu Haka Mazauna Unguwar Sunyi ƙiyasin Sun Gutsire Wa Yara Sama Da Mutum Bakwai, Wanda Har Yaja Mutuwar Ɗaya Daga Ciki.

Bincike Asibiti Ya Tabbatarwa Da Mazauna Unguwar Cewa Matsafan Basa Amfani Da Abun Kaifi Wajen Gutsirewa, Sai Dai Suna Amfani Da Haqoran Bakinsu Wajen Shan Jinin.

Lamarin Dai Yanzu Ya Sawa Iyaye Shakku a Unguwar Wanda Yanzu Yara Sun Rage Zirga – Zirga Saboda Gujin Tsoran Faruwar Hakan.

Sakataren Dawakin Dakata Reporters Wato Shamwilu Muhammad Dahiru Dawakin Dakata Yayi Kira Ga Iyayen Yara Da Su Killace Ƴaƴan Daga Ya Wace , Ya Wacen Banza Har Izuwa Lokacin Da Allah Zai Tona Asiri Masu Yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *