Dakata Facebook Connects 2nd Editions.

Dakata Facebook Connects 2nd Editions Ya Gudana Ne Ayau Lahadi 10 Gawatan Augustan Shekarar 2025 Wanda Taron Ya Gudana Aharabar Taro Na B,m,c Center Dake Nan Kwanar Tifa.
Taron Ya Samu Halatta Manyan Baqi Wadanda Suka Haďa Da Masu Madafan Iko Agwamnati, Dagaci Tare Da Masu Unguwanni, Shuwagabannin ‘Yan Kasuwar Kwalema Dama Na Kasuwar Waya Ta Kwanar Tifa.
Sadiq Muhammad Mai Gatari Jami’in Hudda Da Jama’a Na Rundunar Hana Fatauci Da Miyagun Kwayoyi Na Jihar Kano Yayi Kira Ga Matasa Wadanda Suka Tsunduma Harka Shaye – Shaye Dasu Yiwa Kansu Karatun Ta Nutsu Akan Yadda Rayuwarsu Zata Kasance Gaba.
Ya Kuma Kara Tabbatar Mana Da Cewa ‘Kasashen Dasu Ke Turo Miyagun Kwayoyi Izuwa Kasarnan , Ba Sa Yadda ‘Yan Kasar Su, Su Sha Saboda Sun San Illata.
Ya Kuma Yi Kira Da Babbar Murya Ga Gidan Bola Na Kwalema Game Da Dillolin Kwaya Da Suka Tare Aciki Da Su Guji ‘Daukar Matakin Hukumar.
Muhammad Awaisu Gumel D,P,O Na Dakata Division Yayi Kira Ga Iyayen Yara Tare Da Duk Wasa Kungiyoyi Dasu Dinga Baďa Hađin Kai Yayi Da Suke Gudanar Da Aiki.
Ya Kuma Qara Da Cewa Zaiyi Maraba Da Duk Wata Kungiya Da Zata Tazo Ta Taya Su Aiki Domin Aikin Bana Mutum ‘Daya Bane.
Journalists Shamwilu Dawakin Dakata