
Wasu baƙin ƴanbindiga sun tayar da ƙauyuka da dama a Zamfara’
Al’ummar yankin Bukkuyum a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce wasu baƙin ƴanbindiga sun tarwatsa ƙauyuka da dama a yankin. Ɗanmajalisar jiha da ke wakiltar yankin ya ce wasu baƙin ɓarayi ne daga kasashen waje suke kaddamar da sababbin hare-haren a sassan yankunan kananan hukumomin Bukkuyum da Anka na jihar Zamfara.Honarabul…