Category: nishadi

Ni ne mutum mafi shahara da aka fi caccaka a Nijeriya – Davido
Fitaccen mawakin nan na kudancin Nijeriya David Adeleke wanda aka fi sani da Davido, ya ce shi ne shahararren dan Nijeriya da ya fi fuskantar suka, duba da inda ya fito. Da yake magana a shirin Culture Knock Out podcast, mawakin ya bayyana cewa ra’ayin jama’a ya canza ne bayan an gano cewa ya fito…

Gwamnatin Nijeriya ta ja kunnen ‘Sarkin Mota’ kan tsokanar ma’aikatan gwamnati a bidiyonsa
Gwamnatin tarayya ta gargadi dillalin motoci a Abuja, wanda aka fi sani da Alamin Sarkin Mota, kan yi wa ma’aikatan gwamnati ba’a a cikin bidiyon talla da yake yi. Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA ce ta yi wannan gargadi a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun babban daraktanta, Lanre Issa-Onilu,…

FIFA ta gayyaci mawakiya ‘yar asalin Nijeriya Temilade Opeyemi domin ta yi wasa a gasar FIFA Club World Cup
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta gayyaci mawakiya ‘yar asalin Nijeriya, Temilade Openiyi wadda aka fi sani da Tems, domin gudanar da wasa a gasar da za a fara ta FIFA Club World Cup karo na fatko, wanda zai gudana a filin wasa na MetLife da ke New York na kasar Amurka a ranar…

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 21 cikin tawagar ‘yan wasan Kano a gasar wasanni ta Nijeriya
‘Yan wasan na kan hanyarsu ne ta dawowa gida Kano daga jihar Ogun, inda suka fafata a gasar ta kwallon kafa. Jaridar Daily Nigerian ta ce cikin wadanda hatsarin ya yi ajalinsu akwai ‘yan wasa 17 da mai magana da yawun hukumar wasanni ta jihar Kano Galadima Ibrahim da sauran wasu jami’ai. Kawo yanzu wadanda…

Ba na bakin ciki da nasarar da PSG ta samu a gasar Champions League – Mbappe
Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Faransa, Kyllian Mbappe ya ce ko kadan bai yi bakin ciki da nasarar da tsohuwar kungiyarsa ta kwallon kafa PSG ta samu a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai wato Champion league ba. Mbappe ya bayyana ma ‘yan jaridu gabanin wasan da za su buga a ranar Lahadi cewa,…