Da dumi’dumi: Rasha ta gargadi Amurka da kada ta taimakawa Isra’ila ta hanyar soji kan Iran idan ba haka ba kasar Rasha zata karbi goron gayyatar taimakawa Iran

Da dumi’dumi: Rasha ta gargadi Amurka da kada ta taimakawa Isra’ila ta hanyar soji kan Iran idan ba haka ba kasar Rasha zata karbi goron gayyatar taimakawa Iran. Kasar Rasha ta gargadi Amurka game da baiwa Isra’ila tallafin soji a ci gaba da kai hare-hare ta sama tsakanin Iran da Isra’ila. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sergei Ryabkov ya bayyana cewa irin wannan taimakon na iya “dagula al’amura a gabas ta tsakiya sosai.” Shugaban hukumar leken asirin harkokin wajen Rasha Sergei Naryshkin, ya bayyana lamarin a matsayin mawuyacin hali. Tattaunawar da Amurka ta yi, an bayar da rahoton sun hada da zabin daukar matakin soji a kan cibiyoyin nukiliyar Iran. A baya dai shugaba Trump ya ba da shawarar a kai wa shugabannin Iran hari amma ya yi ikirarin daukar matakin gaggawa. Bayan harin ba-zata da Isra’ila ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran, wanda Rasha ta yi Allah wadai da shi, Iran ta mayar da martani da harin makami mai linzami. Shugaba Putin ya yi kira da a kawo karshen tashin hankalin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *