Daga Zuwa Tambaya An Ɗaura Auren Ɗan Kuda Kabo Da Zainab Abdussalam a Katsina.

An ɗaura auren jarumin Kannywood ɗin nan kuma ɗan siyasa hadimin Sanata Barau Jibrin wato Jamilu Dan Kuda Kabo da amaryarsa Zainab Abdusalam a Katsina.
Ɗaurin auren ya zo ne a Asabar ɗin nan yayin da waliyansu suka je domin tambaya inda aka cimma matsayar ɗaura auren a nan take.
A watan Nuwamban shekarar da ta shuɗe ne, Dan Kudan ya yi rashin uwar gidansa.