Har yanzu duniya na jiran matakin da Trump zai ɗauka kan Iran

Shugaban Amurka, Donald Trump dai har yanzu ya ƙi bayyana ko Amurka za ta shiga hare-haren Isra’ila kan Iran yayin da duniya ke jiran matakin da zai ɗauka.

A lokacin da aka tambaye shi a filin Fadar White House jiya, Trump ya ce, “Zan iya shiga kuma zan iya ƙi.

“Bayan haka, rahotanni sun ce Trump ya amince da shirin kai hari amma yana jiran ko Iran za ta yi watsi da shirin nukiliyarta.

Iran ta shaida wa Majalisar Dinkin Duniya cewa ba za ta yi sulhu a karkashin matsin lamba ba.

Tsohuwar mai ba da shawara kan tsaron ƙasa ta Trump, KT McFarland, ta ce Trump zai iya yanke shawara dab da lokacin da za a ƙaddamar da harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *