Masoyan Ganduje Ne Ke Rububin Gaisawa Da Shi Amma Ba Dukansa Za Suyi Ba, Inji Jam’iyyar APC Ta Jihar Kano

Masoyan Ganduje Ne Ke Rububin Gaisawa Da Shi Amma Ba Dukansa Za Suyi Ba, Inji Jam’iyyar APC Ta Jihar Kano

Jam’iyyar Apc ta jihar Kano ƙaryata labarin cewa wasu ‘yan siyasa sunyi yunƙurin dukan Ganduje a wajan taron jam’iyyar APC a jihar Gombe.

A ranar Lahadi ne dai aka gudanar da taron jam’iyyar APC na shiyar Arewa maso Gabas a jihar Gombe, inda hayaniya ta ɓarke sakamakon rashin ambatar Kashim Shettima da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Gamduje yayi kan zaɓen 2027 mai zuwa.