Shugaban Hafsoshin Tsaron Iran,Manjo Janar Abdoulrahim Mousavi Ya Bayyana Cewa Har Yanzu Gargaɗi Suke Yiwa Kasar Israel Basu Fara Yaqi Ba Tukunna

Shugaban hafsoshin tsaron Iran, Manjo Janar Abdolrahim Mousavi, Ya bayyana cewa Har Zuwa yanzu Gargaɗi Suke yiwa ƙasar Isr@’ila Basu fara yaƙi Ba Tukunna. Sannan ya tabbatar da cewa Manyan Hare-hare Suna Nan Zuwa Nan gaba ga Isr@’ila

Shugaban hafsoshin tsaron Ir@n, Manjo Janar Abdolrahim Mousavi, ya bayyana cewa hare-haren da Iran ta kai tun daga ranar Juma’a sun kasance gargadi na hana kai hari, amma ainihin ramuwar gayya zai fara ne nan ba da jimawa ba.Manjo Janar Mousavi ya ce hare-haren da aka kai zuwa yanzu sun kasance ne don gargaɗi, amma an shirya aiwatar da ainihin matakan ramuwar gayya nan kusa.

Ya ce gwamnatin Isr@’ila ta karya dukan dokokin ƙasa da ƙasa, tana ci gaba da kisan kusan ’yan jarida 300 a Gaza da Lebanon, sannan kuma ta kai hari kan ofishin gidan talabijin na Iran (IRIB) domin toshe muryar gaskiya.Ya bayyana hakan ne dangane da harin da Isr@’ila ta kai kan hedikwatar IRIB da ke Tehran a ranar Litinin.

Babban kwamandan ya ƙara da cewa mazauna yankunan da Isra’ila ke mamaye, musamman Tel Aviv da Haifa, su gaggauta barin waɗannan wurare don kare rayukansu, kada su fada cikin muguwar manufar Netanyahu.

Ya kuma bayyana cewa mutanen duniya da ke goyon bayan ‘yanci za su ga cewa al’ummar Iran, tare da jagorancin rundunar sojoji, za su rama jinan shahidan da aka kashe.

Shamwilu Dawakin Dakata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *