A karon farko Nijeriya za ta fara fitar da tataccen man fetur zuwa nahiyyar Asia kamar yadda wata majiya daga Matatar Dangote ta sanar.
Muna sayar da kayanmu ne ga waɗanda suka yarda su ba mu farashi mafi yawa. Majiyar ta ce wani jirgin ruwan dako mai ɗauke da tan 90,000 na man fetur zai yi jigilar daga Matatar Dangote da ke Nijeriya zuwa nahiyar Asia. Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ambato majiyar wadda ta buƙaci a sakaya…