TIRƘASHI: Wani lauya ɗan ƙasar Kenya mai suna Dola Indidis ya shigar da ƙara a Kotun Duniya (ICJ) yana zargin Isra’ila da Italiya da hannu a kisan Yesu Almasihu da ya faru shekaru fiye da 2,000 da suka wuce.

Indidis ya ce kisan da aka yi wa Yesu bai bi ƙa’idojin shari’a ba, inda ya bayyana cewa an yanke masa hukuncin kisa ba tare da adalci ba. Ya nemi kotun ta sake duba shari’ar bisa hujjar cewa kasashen biyu sun gaji tsarin shari’ar daular Roma, wacce ta ɗaure ta kuma gicciye Yesu.
Ƙarar ta haɗa da sunayen tsofaffin shugabanni da suka haɗa da Pontius Pilate, King Herod, Judas Iscariot, da Emperor Tiberius, duk a matsayin waɗanda suke da hannu a haramtacciyar shari’ar.
Sai dai Kotun Duniya ta ƙi karɓar ƙarar, tana mai bayyana cewa ba ta da ikon shari’a a irin wannan lamari, kasancewar ICJ na sauraron rikice-rikice ne kawai tsakanin ƙasashe, kuma da izinin su.