Wasu baƙin ƴanbindiga sun tayar da ƙauyuka da dama a Zamfara’

Al’ummar yankin Bukkuyum a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce wasu baƙin ƴanbindiga sun tarwatsa ƙauyuka da dama a yankin.
Ɗanmajalisar jiha da ke wakiltar yankin ya ce wasu baƙin ɓarayi ne daga kasashen waje suke kaddamar da sababbin hare-haren a sassan yankunan kananan hukumomin Bukkuyum da Anka na jihar Zamfara.Honarabul Hamisu A.
Faru Nasarawa Burƙullu, mai wakiltar Bukkuyum ta Kudu a majalisar dokokin jihar Zamfara ya ce ƴanbindigar sun kashe sama da mutum 20.
Ya ce al’amarin ya kai maƙura, har yana neman hana gudanar da harkokin noma a daminar bana a yankunan da abin ya shafa.
“Akwai baƙin ɓarayi a dajin Gando kuma sun ce yankin Bukkuyum ba za a yi noma ba,” kamar yadda Hon Hamisu Faru ya shaida wa manema labarai
Ya ce al’ummar yankin musamman Ruwan Rana da Bukkuyum ta arewa suna cikin tashin hankali kuma mutane da dama ne ke gudun hijira.
“Ƴanta’addan sun zo da yawa sun kashe mutane sun kuma kwashi shanu da raƙuma da awakai,” in ji shi.Ɗanmajalisar ya yi iƙirarin cewa kusan kashi 70 na mazaɓun da yake wakilta suna ƙarƙashin ikon ƴanbindigar.
Ya ce lamarin ya fi ƙamari a yankin Adabka da Kairu da Kyaram da Gwashi da ƙauyukan Ruwan Rana da Ruwan Jema da Gasa Hula Ƙurfar Danya da Barayar Zaki da Rafin Gero, duka babu zaman lafiya.
“Ƴanta’adda su ne hakimai, kuma su suke yin hukunci,” in ji shi.
Ɗanmajalisar jihar ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha su kawo masu ɗauki domin yaƙar ƴanbindigar don al’umma su samu su yi noma.
Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin arewa maso yammaci da ke fama da matsalar ƴanbindiga masu fashin daji.
Ƴanbindigar suna kai farmaki ƙauyuka, su kashe, su saci mutane tare da kone gidaje bayan sun wawushe kayan mutane.